Yadda aka sace Limamin Masallacin Senchi

Limamin Masallacin Juma'a na Senchi Alh Mande Kibiya dattijo ne da ya gamu da ibtila'i na masu sace mutane domin su karbi kudin fansa.
Amma wani bincike da muka gudanar ya nuna cewa wadanda suka sace shi wasu yara ne al'ummar Fulani wadanda suka san daji matuka kuma wannan shi ne karo na biyu da aka sace shi .

Haka zalika bayanai sun nuna cewa bayan da aka sace shi daga gidansa a garin Kibiya an kai shi wani daji ne a cikin jihar Zamfara.

Jihar Zamfara dai ta zama matattara ga ayyukan garkuwa da mutane da harkar ta'addanci na kisan bayin Allah da basu ji kuma basu gani ba.

Amma yanzu haka mahukunta sun dauki tsattsaran matakan tsaro a jihar Zamfara domin ganin an shawo kan irin ayyukan ta'addanci da suka auku a baya.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN