Fitaccen Jarumin wasan finafinan Bollywood Salman Khan ya samu yanci bayan wata Kotun daukaka kara ta bayar da belinsa ranar Asabar.
Alkalin Kotun Ravindra Kumar Joshi ya bayar da belin Salman a kan Rupee 50.000 tare da samun wanda zai tsaya masa kafin ya bar Kurkukun da aka tsare shi a garin Jodhpur a yammacin India.
Bayan an sake Salman Khan nan take kide-kide raye-raye da bushe-bushe suka kaure a waje daga harabar Kotun wanda masoyansa suka yi ta shewa suna cewa "Muna kaunar ka ,kuma muna tare da kai Salman Khan!".
Bayan haka Salman ya zarce kai tsaye zuwa filin jirgin sama inda ya wuce zuwa garinsa na haihuwa Mumbai tare da kanwarsa Alvira da Arpita wadanda suke a cikin Kotun tsawon lokacin zaman ta.