• Labaran yau


  Yadda aka saci asirin mutum miliyan 2.7 masu amfani da Facebook

  Kamfanin Facebook na fuskantar damuwa sakamakon wata badakala na satar sirri na masu amfani da shafin a nahiyar turai wanda ya shafi mutum miliyan 2.7 wanda aka yi wa lakabi da Cambridge Analytica Scandal.

  A gefe daya kuma kamfanin na Facebook za ta samar da dama wanda za a saka yanayi da mai amfani da shafin zai iya goge sako da ya aika ta hanyar Manhajar aika sako na Messanger komin dadewarsa.

  Wannan ya biyo bayan yadda aka gano cewa shugaban kamfanin na Facebook Mark Zuckerberg yana goge miliyoyin sakonni da ya aika wa masu amfani da shafin a Duniya amma kuma ba a samar da wannan damar ga masu amfani da shafin ba.

  Yanzu haka Facebook za ta samar da wannan dama ga masu amfani da shafin domin su sami damar da za su iya goge sakonni da suka aika a can baya komin dadewarsa.

  Kididdiga ya nuna cewa fiye da mutum biliyan 2.2 ne ke amfani da shafin Facebook a fadin Duniya.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda aka saci asirin mutum miliyan 2.7 masu amfani da Facebook Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama