Mutum hudu ne aka tabbatar sun mutu yayin da goma sha tara suka sami raunuka a wani mumunar hadarin mota da ya auku wanda ya rutsa da motoci da dama a kan hanyar Bauchi daga Dogon Danmarke a karamar hukumar Wudil da ke jihar Kano.
Kakakin hukumar kashe gobara na jihar Kano Alh. Saidu Muhammed ya ce hadarin ya faru da misalin karfe 10:44 na safe ranar Juma'a .
Muhammed ya ce samun labarin aukuwar hadarin ke da wuya sai suka tura jami'an su wadanda nan take suka shiga aikin taimaka wa wadanda lamarin ya rutsa da su a cikin motoci uku da suka hada da Toyota Hummer,
SA 297 GME; Golf, SSP 134 ES; da Sharon Golf, SA 158 PAT wadanda suka yi karo da juna a hadarin.
Tuntube mu ko aiko Labari zuwa
isyakulabari@gmail.com
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001.
Shiga cikakken shafinmu.
www.isyaku.com