Yansanda a birnin Kolkata na kasar India sun kama wani mutum mai shekara 43 bayan an gano gawar mahaifiyarsa da ya boye a cikin wani Firij har tsawon shekara uku domin ya dinga karbar panshon ta kowane wata ta hanyar yin amfani da zanen babbar yatsar hannun ta.
An gano haka ne bayan yansanda sun bankado yadda aka boye gundulallen jikin tsohuwar ranar Alhamis
Mataimakin kwamishinan yansanda DC Nilanjan Biswas ya ce an ajiye gawar Bina Mazumdar ne tun 2015.
.
Haka zalika yansanda sun ce suna tsare da wanda ake tuhuma Subhabrato Mazumdar wanda ma'aikacin gwamnati ne.
Tuntube mu ko aiko Labari zuwa
isyakulabari@gmail.com
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001.
Shiga cikakken shafinmu.
www.isyaku.com