Kiraye ga Sanata Dino Melaye, masu zabe sun ce an yi coge a sunayensu - Bidiyo

Al'ummar Mazabar Sanata mai wakiltar Kogi ta yamma watau Dino Melaye sun ce akwai coge da badakala a jerin sunaye da aka lissafta a takardun kiraye da hukumar INEC ke tantancewa. Da yawa daga cikin jama'a sun ce su fa basu sa hannu ba amma an sa hannu a gurbin su.

Haka zalika wasu sun yi zargin cewa hatta sunayen wadanda suka mutu a 2016 zuwa 2017 sunayen su sun fito kuma an sa hannu a madadin su.

Da yawa daga cikin jama kuwa sun nuna goyon bayan su ne ga Sanata Dino Melaye inda suka ambato cewa Sanata ne mai gaskiya wanda ke bayar da nagartaccen wakilci ga jama'arsa.

Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN