B-kebbi: Kungiyar 4+4 ta bayar da motoci 124, Isuhu Haruna ya caccaki BBSO

Kungiyar 4+4 mai karadin ganin an sake zaben shugaba Muhammadu Buhari da Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Abubakar Bagudu ta gudanar da babban taron hadin kai tare da bayar da motoci guda 124 ga masu yi masu yakin ganin an yi nassara a zaben 2019.

Filin wasa na Haliru Abdu da ke garin Birnin kebbi ya cika matuka da jama'a magoya bayan jam'iyar da suka zo domin karramawa ga jam'iyar APC na jihar Kebbi da Najeriya gaba daya,

Amma a nasa jawabi a wajen taron, Isuhu Haruna Rasheed wanda shi ne Mai ba Gwamnan jihar Kebbi shawa kan harkokin Siyasa ya caccaki tsarin mai taimaka wa Gwanman jihar Kebbi watau P.A bisa nashi tsarin tafiyar ta Buhari Bagudu Support Organization BBSO yana mai cewa tsarin tafiyar 4+4 shine a kan tsari.

Isuhu Haruna ya kara da cewa 4+4 hadaddiyar tafiyace ta kungiyoyi da suka hade kuma take tafe da jagorancin mutane kamar su Abba Aliero, Ibrahim Bagudu da sauransu.

Shi kuma  a nasa jawabi, Sanata Adamu Aliero ya bayyana cewa abin da jam'iyar APC take bukata a jihar Kebbi da Najeriya shi ne hadin kai domin ganin an ci nassara a lamari da aka sa a gaba.Ya kuma bukaci jama'a su daina yin ababe da zai iya kawo rarraba a tsakanin magoya bayan jam'iyar APC.

Daga bisani Alh, Bello Bagudu ya ce yanzu ba lokaci ne da magoya bayan jam'iyar APC za su dinga ganin laifin juna bane, amma lokaci ne da ya kamata a hada kai tare da bin doka da oda domin ganin an ci nassara.

Manyan mutane da dama ne suka bayar da motoci a wajen taron wadanda suka hada da Abba Aliero mota 16, kungiyar Chiyamomin kananan hukumomi ALGON na jihar Kebbi mota 21 watau mota 1 daga kowace karamar hukuma, SSG Babale Umar mota 5, Kabiru Kamba mota 6, Minista Chika Malami mota 6 tare da Miliyan 3 da sauran su.

Daga cikin manyan baki da suka halarci taron sun hada da Alh. Umarun Kwabo daga jihar Sokoto, Sanata Adamu Aliero, Wakilin Ministan sharia kuma Attoni janar na Najeria Abubakar Chika Malami, Abba Aliero, Sakataren Gwamnatin jihar Kebbi Umar Babale da sauran manyan baki daga ciki da wajen jihar Kebbi.

Daga Isyaku Garba.

Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN