Wani bawan Allah ya sami cikawa a Masallaci yayin da yake sallah a kasar Jordan.Wani hoton bidiyo ya nuna yadda dattijon ya yanke jiki a tsayuwar Sallah kuma ya yi sujada kai tsaye, daga nan kuma bai mike ba.
Wannan lamarin ya faru ne a yankin gabacin Aghwar a yankin gwamnatin Irbida a kasar Jordan.
Na'urar CCTV na Masallacin ne ya dauki hoton bidiyon wanda aka yi ta labartawa a gidajen talabijin na kasar Jordan.
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001.
Shiga cikakken shafinmu.
www.isyaku.com