Shugaban kasar
Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya ziyarci takwaransa na Koriya ta Kudu Moon
Jae-in lamarin da ake ganin zai kafa tarihin samar da zaman lafiya da
lumana a tsakanin kasashen biyu.
Shugabanin
biyu sun gana a Panmunjom da suka kira kauyen zaman lafiya domin
tattunawa akan samar da zaman lafiya a tsakaninsu inda shugaba Kim ya
rataba hannu a cikin littafin lumana da aka bude.
Kim ya bayyana cewar yanzu mun fara daukar matakan samar da zaman lafiya a tsakanimu kuma zamu mutunta matakan da zamu dauka.
A
watan Febrairu shugaba Kim ya tura wasu tawagar da suka kunshi har da
kaunarsa Kim Yo-jong zuwa Koriya ta Kudun inda suka fara tattauna samar
da zaman lafiya tsakanin kasashen biyu.
A
taron zaman lafiyar, shugaban Koriya ta Arewa ya bayyana irin farin
cikinsa akan ganawa da takwaransa na Koriya ta Kudu da yayi ,inda ya
kara da cewa yanada yakinin taron zai haifar da da mai ido.
Shugabanin
biyu sun godewa juna akan gudanar da taron inda dukkaninsu suka nuna
farin jikinsu akan matakan samar da lumana a tsakaninsu.
Moon
ya bayyana cewar al'umar kashashen biyu dama duniya baki daya sun
karkata kunnuwansu da idanuwansu zuwa Panmunjom domin kowa na bukatar
nasarar taron da ake gudanarwa.
Hakika, nasarar wannan taron zai kasance tamkar wata babbar kyauta ga al'umar kasashen dama duniya baki daya.
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Daga TRT