Kalli bidiyon yadda aka yi fashi a Bankin Offa na jihar Kwara

Wani hoton bidiyo ya bayyana a shafukan yanar gizo daga na'urar CCTV na wani Banki wanda ake zargin ya nuna yadda yan fashi da makami suka yi fashi a Bankin da ke garin Offa na jihar Kwara ranar Alhamis da ya gabata.

A wannan hoton bidiyon an ga wata mata rike da yar karamar yarinya tana shiga Bankin yayin da wasu mutum biyu da ke tsaye a wajen ATM suka ruga da gudu bayan yan fashin sun fara harbin kan mai uwa da wabi daga wajen Bankin.

Rahotanni sun ce kimanin mutum 30 ne aka kashe a fashin da ya dauki awa biyu ana gudanarwa a garin na Offa ba tare da samun daukin gaggawa daga jami'an tsaro ba.Kimanin jami'an yansanda bakwai ne ake fargaban sun mutu a wannan fashi da makami na garin Offa.



Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN