Shugaban rundunar kasa na sojin Najeriya Lt. Gen Tukur Buratai ya kafa wani kwamiti wanda zai yi bincike a kan zargi da tsohon janar na soji T.Y Danjuma ya yi dangane da rikicin jihar Taraba.
A watan da ya gabata ne T.Y Danjuma ya zargi sojin Najeriya da aikata ba daidai ba a Taraba da Benue da kuma wasu sassa na Najeriya.
Danjuma ya zargi sojin Najeriya da mara wa masu kisan mutane baya a jihar Taraba tare da nuna goyon baya ga wani bangare a rikicin na Taraba.
Gen. Baratai ya ce wajibi ne a gudanar da bincike domin a tsabtace mutunci da darajar rundunar sojin Najeriya kuma bai kamata a yi fatali da irin wannan zargi ba.
Tuntube mu ko aiko Labari zuwa
isyakulabari@gmail.com
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001.
Shiga cikakken shafinmu.
www.isyaku.com