Jihar Kebbi: Ka san dalili da ya sa Chiyaman na Koko ya yi murabus ?

A mako da ya gabata ne shugaban karamar hukumar Koko Besse watau Alh. Shu'aibu Ibrahim ya yi murabus na bazata daga mukaminsa na shugabancin karamar hukumar, lamari da ya ba mutane mamaki matukar gaske.

Bisa bukata da masoyan shafin ISYAKU.COM suka yi na sanin sahihin gaskiyar abin da ya faru kafin shugaban ya sauka daga mukaminsa.Mun gudanar da bincike akan lamarin.

Da farko dai binciken mu ya nuna cewa babu wata matsala tsakanin tsohon chiyaman Shu'aibu da Kansilolin sa. Na biyu kuma babu wata matsala tsakanin sa da Gwamna Atiku Abubakar Bagudu ko ahalin sa. Na uku baya da matsala da jam'iyar APC na jihar Kebbi da na kasa gaba daya ko shugabancin jam'iyar ta APC.

Binciken mu har ila yau ya nuna cewa Kansiloli da jama'ar gari basu ji dadin yadda tsohon chiyaman ya yi murabus haka kawai ba ganin cewa jama'a ne suka sha wuya a cikin rana suka zabe shi.

Amma majiyar mu ta tabbatar mana cewa Alh. Shu'aibu Ibrahim ya ce har abada yana tare da Gwamna Atiku Bagudu tare da ahalin sa, da jam'iyar APC kuma a shirye yake ya bayar da nashi gudunmuwa a kowane lokaci bukatar haka ta taso.

Haka zalika majiyar ta ce Alh.Sha'aibu ya yi murabus ne bisa rabin kansa kuma ba tare da niyyar ya saba ma wani ba face domin ra'ayin kanshi kawai.

Wannan ya kawar da jita-jita da ke zagayawa a shafukan intanet na zargin matsala ko ba daidai ba tsakanin Alh. Sha'aibu da wasu masu iko ko fada a ji a jihar Kebbi.

Daga Isyaku Garba a Birnin kebbi

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN