• Labaran yau


  2019: Ko shugaba Buhari ya yi amai ya lashe kenan ?

  Mai taimaka wa shugaba Muhammadu Buhari ta fannin sadarwa Femi Adesina ya ce zance da shugaban ya yi a shekara ta 2011 cewa zai yi shugabanci ne na shekara hudu kacal idan ya ci zabe baya da tasiri a yanzu.

  A wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels TV da safiyar Talata, Adesina ya ce shugaba Buhari ya yi wannan furuci ne a waccan lokaci kuma ya yi takara ya fadi a waccan zaben.

  Ya kara da cewa a wannan lokaci ai shugaban bai yi wannan alkawari ba. Kuma nassarar lashe zabe a shekara ta 2015 ne ba 2011 ba.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: 2019: Ko shugaba Buhari ya yi amai ya lashe kenan ? Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama