Hukumar da ke kula da hanyoyin gwamnatin tarayya a Najeriya reshen jihar Kebbi FERMA ta ce ta fara gyara hanyoyin da suka lalace na gwamnatin tarayya a garin Argungu, Ribah da Arewa da kuma hanyar jami'ar tarayya a Birnin kebbi.
Shugaban hukumar na reshen jihar Kebbi Riwanu Usman ya shaida wa wakilin kamfanin dillancin labarai na Najeriya yayin da yake zantawa da shi ranar Juma'a a Birnin kebbi.
Ya ce hukumar ta dukufa domin ganin ta gyara hanyoyin da suka lalace wanda ya hada da yin ciko a wajen da hanya ta fashe tare da cika ramu a hanyoyin .
Haka zalika ya ce hukumar ta kammala hanya mai tsawon kilomita 2.5 a jami'ar tarayya Birnin kebbi da kuma hanya mai tsawon mita 14 a Dirin Daji
Tuntube mu ko aiko Labari zuwa
isyakulabari@gmail.com
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001.
Shiga cikakken shafinmu.
www.isyaku.com