Shugaba Buhari ya ce kimanin kashi 60 na yawan yan Najeriya matasa ne kuma galibin su sukan zauna ne ba tare da yin wani aiki ba yayin da suke jiran gwamnati ta tallafa masu kyauta daga kudin man fetur.
Alh. Atiku Abububakar ya ce ba zai taba yin irin wannan kalamai ba cewa matasan Najeriya ragwaye ne.
Atiku ya ce "akwai dubu dubatan matasa a fadin Najeriya da suke yi mani aiki sakamakon haka ake ta samun nassarorin rayuwa. Ba man fetur ne kadai madogaran arzikin Najeriya ba. bugu da kari ai akwai matasan mu da suka kirkiro Nollywood domin nishadantar da jama'a wanda babban nassara ne".
Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com