Duk wanda ke kuka cewa akwai yunwa ya je ya yi aiki - Garba Shehu

Mai taimaka wa shugaba Muhammadu Buhari kan harkokin watsa labarai Mal. Garba Shehu ya ce Gwammnatin Buhari ta yi ayyuka domin taimaka wa jama'a sakamakon haka jama'a na kokawa akan yunwa,yace duk wanda ke kukan cewa akwai yunwa ai sai ya je ya yi aiki.

Garba Shehu ya yi wannan jawabi ne a yayin da yake amsa tambaya a wani shiri da ya bayyana a Ben TV. Ya ce wannan gwamnati tana taimaka wa gajiyayyu da masu fama da matsanancin talauci da N5.000 a kowane wata lamari da babu wata gwamnati da ta shude ta yi.

Ya kuma kara da cewa tun lokacin da shugaba Buhari ya hau mulki ya mayar da hankali wajen samar da ababen more rayuwa ga talakan Najeriya ta hanyar amfani da kashi 30 na kason kasafin kudi.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN