An kama safeton dansanda da ya mari budurwa sakamakon cacan baki

Kwamishinan yansanda na jihar Lagos ya bayar da umarnin kama wani safeton yansanda mai suna Lawal Murtala sakamakon marin wata yarinya mai suna Bibi bayan wani faifen bidiyo da ke zagaywa a shafukan intanet ya nuna yadda dansandan ya waska ma Bibi mari.

Bibi ta zargi dansandan da dukan mutane a cikin wata motar bus a kan hanyarsa daga Obalande zuwa Dopemu akan hanyar Agege.

Kwamishinan yansanda na jihar Lagos ya ba DPO na Dopemu umarni ta kama safeton kuma ta mika shi ga sashen hukumar masu kula da da'ar jami'an yansanda watau Provost a hedikwatar yansanda na jihar Lagos domin gudanar da bincike.

A post shared by Bibi Anne (@beebee_anne) on
Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN