• Labaran yau


  Dan Majalisar wakilai a jihar Taraba ya sha ruwan duwatsu a hannun matasa

  Matasa a jihar Taraba sun yi ma dan Majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Bali/Gassol Hon.Garba Hamman Julde ruwan duwatsu bisa  zargin cewa dan majalisar ya yi watsi da su tun lokacin da ya je Fadar Majalisa da sunan wakiltar su.

  Hakan ya faru ne a lokacin da Dan Majalisar ya raba babura 11 tare da mota 1 ga shugaban jam'iyar APC na karamar hukumar Bali ranar Asabar, sai matasa da suka harzuka suka afka mashi da ihu da jifa bayan ya gama jawabinsa yayin da ya ke kakarin mika makullan baburan.

  Tuni dai wasu jama'a tare da jami'an tsaro suka ceto Dan Majalisar ta hanyar ba shi kariya zuwa wani waje.


  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Dan Majalisar wakilai a jihar Taraba ya sha ruwan duwatsu a hannun matasa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama