Dole Miyetti Allah ta gano Fulani da ke kisa cikin wata 2 -- Sarkin Musulmi

Shugaban Majalisar koli na harkokin addinin Musulunci a Najeriya kuma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar ya ba sabon zababben shugaban kungiyar Miyetti Allah na Najeriya wa'adin wata biyu ya binciko tare da gano ko su waye suke kashe kashe da ake cewa Fulani ne a kasarnan.

Sarkin Musulmi ya yi wannan bayani ne yayin da yake jawabi a wajen taron nadin sabon shugaban na Miyetti Allah a Sokoto ranar Talata.

Ya kuma bukaci shugaban na Miyetti Allah ya tabbatar ya tantance ko Fulani ne suke wannan kashe-kashe da gidajen watsa labarai suke alakanta Fulani da aikatawa ko akasin haka ganin cewa an sha kashe al'ummar Fulani har ma a kwashe dabbobinsu bayan an kashe su a kasar nan amma babu wata kafar watsa labarai da ta bayar da muhimmanci a wajen watsa wannan labari.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN