Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Ka san me Sanata Shehu Sani ya yi bayan an sace sandar girma a Majalisa ?

Bayani da muka samu daga Majalisar Dattawa ya nuna cewa bayan wadansu yan daban siyasa sun sace sandar girma na Majalisar Dattawa a ranar Laraba, Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya cire bel na wandonsa ya saka a madadin sandar girman kuma sakamakon haka sauran Sanatocin suka aminta cewa Majalisar ta ci gaba da zamanta.

Sakamakon haka Majalisa ta ci gaba da zamanta kuma gaba daya Sanatoci sun yi Allah wadai da wannan lamari. Sanata Omo-Agege wanda ake zargi da jagorantar yan daba zuwa zauren Majalisar tuni ya fada hannun yansanda bayan sun shigo harabar Majalisar kuma suka yi awom gaba da shi.

Wata sanarwa da ta fito daga Kakakin Majalisar Dattawa Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ya ce sace wannan sandar girma na Majalisar Dattawa cin amanar kasa ne .

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com