• Labaran yau


  Kotu ta daure matashi shekara 2 sakamakon satar tumaturin gwango

  Wata Kotun Majistare a Oredo na jihar Edo ta daure wani matashi dan shekara 32 mai suna Austine Ibe tsawon shekara biyu a gidan Kurkuku bayan ta same shi da laifin satar katon 75 na tumaturin gwangoni wanda aka kiyasta kudinsa akan N315.600.

  Wanda aka kama da laifin ya aikata laifin ne ranar 14 ga watan Oktoba 2017 a gidan wani Mr Paul Okafor  wanda ke lamba 4 unguwar Butcher a garin Benin.

  Majistare F.E Ekhere ya yanke wa  Austine hukunci ne ba tare da bayar da damar biyan tara ba.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kotu ta daure matashi shekara 2 sakamakon satar tumaturin gwango Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama