Da bazar waye Gwamna Atiku Bagudu ke mulki a jihar Kebbi 4+4 ko BBSO ?

Sakamakon kalamai na zagi da kalubale ga P.A na gwamnan jihar Kebbi Faruku Enabo da mai ba gwamnan jihar Kebbi shawara kan harkar siyasa ya yi a taron kungiyar 4+4 da aka yi a garin birnin Kebbi ranar Lahadi. Lamarin ya zaburar da dimbin masoyan Enabo wadanda suka karbe ragamar shafukan sada zumunta na Facebook da hotunansa tare da ambata kalamai na jinjina da nuna goyon bayansu gare shi a zaurukan Dandalin siyasar Kebbi da Kebbi social Media Forum.

Wani abin da ke daure kai shi ne yadda wadannan kalamai suka fito daga bakin mai ba gwamna shawara a kan harkar siyasa wanda binciken mu ya nuna cewa surukin shi P.A Enabo ne domin Enabo yana auren diyar kanin sa ne. Amma sai ga wadannan kalamai sun fito daga bakin surukinsa.

Amma da bazar waye gwamna Atiku Bagudu ke damawa a jihar Kebbi? 4+4 wacce hadin gambizar mutum 7 ne irin su Abba Aliero da kanin gwamna Ibrahim Bagudu ko kuwa BBSO wanda ta hada da P.A Faruku Enabo da Dan Fari Dakingari da sauransu ?.

Bisa dukkan alama an dade ana boye wata matsala da wutar ta ke ta ci a karkashin kasa har sai ranar Lahadi da Isuhu Rasheed ya bude tukunyar girki dalili da ya sa makwabta suka ji kamshin girki da ake yi a siyasar jihar Kebbi.

Binciken mu ya nuna cewa Gwamna da Mataimakinsa basu je wajen taro na 4+4 ba haka zalika a taro da BBSO ta gudanar a babban sakatariyarta kwanakin baya Gwamna da mataimakin sa basu halara ba. Haka zalika binciken mu ya tabbatar cewa Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Samaila Yombe ne ya dauki nauyin gyara tare da yi ma ofishin BBSO penti, kuma shugabannin kananan hukumomi 21 da ke jihar Kebbi suna karkashin 4+4.

Amma idan ba da bazar Gwamna Bagudu ba babu yadda za a yi P.A ya yi kyautar ta hanyar bayar da taimako ko gudunmuwa ta Naira miliyan 10 kai tsaye a wajen taro balle kyautar Naira miliyan daya da yake yi babu iyaka kamar yadda bayanai suka bayyana a shafukan sada zumunta wadanda magoya bayansa ke rubutowa tare da saka hotuna.

Wannan ya zama wajibi Gwamna Bagudu ya sa baki domin ya kashe wutar wannan murhu, domin idan har aka kyale wannan wutar ta ci gaba da ci a karkashin kasa, lallai zuwa gaba za ta rikide zuwa katuwar gobara da Gwamna Bagudu da hadimansa ba za su iya kashe wutar ta ba a jihar Kebbi karkashin jam'iyar APC mai mulki a yanzu. Yanayi da zai iya haifar da sakamako kamar na jihar Kogi da Kaduna tare da jawo rarraba da mumunar gaba tsakanin magoya bayan jam'iyar APC a jihar Kebbi.

Daga Isyaku Garba.

Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN