Wannan lamarin kamar almara, wai yadda ta kasance a
sahihancin yadda aka bari bango ya tsage Kadangare ya sami wurin shiga a
kan neman Duniya....MULKI a jihar Kebbi.Hausawa sun ce babu ruwan Kifi
da Kaska!...ka ji karfin hali. Ya kai dan jihar Kebbi wanda ke kaunarta
da neman kare muradun ta, ko ka san cewa Igbo ne ke kalubalantar kujerar Gwamnan jihar Kebbi a kan zaben 2015,kujerar Sanata Abubakar Atiku Bagudu ?.
Abin da ban mamaki,shin kwangilar wannan Igbo
aka yi domin wulakanta darajar jihar Kebbi ta hanyar yin amfani da shi
ko kuma gazawa ne daga bangaren wadanda suka dauke shi kwangila domin ya
yi wannan aiki?.
Yayin da jihar Kebbi da Sarakunan ta masu Alfarma suka karrama yan kabilar Igbo ta hanyar ba su sarautar gargajiya kamar Mukamin gargajiya na Dan jikan Gwandu da Mabudin Zuru duka Igbo ne aka ba. Amma yan jihar Kebbi nawa ne aka ba sarautar gargajiya a kasar su ta Igbo?
Yayin da aka jiyo Gwamna Atiku Abubakar Baguda a
kafafen labarai ya ce "za su kare kasancewar Najeriya kasa daya da digon
jinin su na karshe" sai ga Igbo ya dukufa ka'in da na'in wai
ala tilas Dan Bagudu bai cancanta ba a zabe da aka yi a jihar Kebbi
wacce ba kasarsa ba bai taba zuwa jihar Kebbi ba amma wai shi ne ya
shigar da kara akan lamarin jihar Kebbi har da takarkarewa ala tilas wai
sai ya jagula kwanciyar hankali a jihar Kebbi ta hanyar shari'a.
Lamarin da daure kai ganin cewa da shi Gwamna Sanata
Atiku Abubakar Bagudu da Janar mai murabus Bello Sarkin Yaki dukansu yan
garin Birnin kebbi ne, kuma 'yan jihar Kebbi.Shin ta yaya Igbo ya zama uban garke a wannan sha'ani ? kenan akan neman MULKI har za a iya yin kwangilar Igbo
domin ya jagula harkokin jihar Kebbi da sunan neman adalci a yanayi da
su yan jam'iyar adawa na jihar Kebbi ba su yi ba da kan su ?.
Sharhi Daga Isyaku Garba
Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Tags:
BIRNIN-KEBBI