Yansanda a jihar Kebbi sun kama mai sayar da bindigogi da bindiga 11

Rundunar yansanda na jihar Kebbi ta kama wanda ke kera mugan makamai tare da sayarwa .Kwamishinan yansanda na jihar Kebbi Mr.Ibrahim M. Kabiru ya shaida wa manema labarai haka ranar Laraba a Birnin kebbi.

Rundunar ta kama wani mai suna Abu Alkali wanda ake wa inkiya da 'Wizi" a Unguwar-Dansanda a garin Bena da ke karamar hukumar mulki ta Danko/Wasagu wanda shi ne ke sayar da bindiga mai baki 2 (double barrel) akan N6.000 yayin da mai baki daya yana sayarwa akan N3.000.An kama shi da bindigogi daban-daban guda 11 a ranar 17 ga watan Fabrairu da misalin karfe 4:30 na yamma.

Amma a nashi jawabi Abu Alkali cewa yayi shi dan banga ne (Vigilante) kuma jama'arsa ce suka bukaci a sayo bindigogin a Mairairai, amma lokacin da ya kai yansanda wajen wanda yake kera bindigogin sun tarar cewa ya riga ya tsere.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN