• Labaran yau


  Sajen yarsanda ta sha duka a hannun wata karuwa a garin Lagos


  Rahotanni daga jihar Lagos sun nuna cewa wata 'yarsanda mai mukamin Sgt. wacce ke aiki a rundunar yansanda na D a Mushin Ihuema Njoku ta sha duka a hannun wata Karuwa Cherish John yayin da yarsandar ta je  Hotel Continental  domin gudanar da aiki, amma bayan musayar yawu tsakanin karuwa Cherish da yarsaanda Ihuoma sai karuwa ta kwada mata kwalbar giya kuma ta yaga mata kaki.

  PM Express ta labarta cewa dalilin da ya jawo wannan matsala shi ne yarsandar ta shiga Hotel din ne daidai lokacin da Karuwai ke neman Maza da za su kwanta da su su basu kudi da yamma, kwatsam sai ga yarsanda da Karuwai suka zarge ta da kawo masu cikas a ko da yaushe yayin da suke sana'ar su ganin cewa Manajan Hotel din yana yin abin da ya kamata.

  Daga bisani yarsanda ta dawo da karin jami'an tsaro aka kama Karuwar kuma aka gurfanar da ita a gaban Kotun Majistare a Isolo bisa tuhumar hada baki a aikata laifi,cin zarafin ma'aikaciya da katsalandan a aikin dansanda. Karuwa dai bata amsa laifin ta ba. Sakamakon haka Alkalin Kotun ya bayar da ita beli akan N100.000.

  An tasa keyar Karuwar zuwa gidan Kurkuku kafin ta cika ka'idar belin ta.Amma Karuwar ta ce zance fa ba haka yake ba, domin dai bayan yarsanda ta shigo sai Karuwai suka harzuka ganin cewa yarsandar za ta bata masu kasuwa,daga nan sai Karuwa Cherish ta bukaci ta gaggauta gudanar da aikin ta domin su ma su nemi nasu abinci.

  Daga nan ne cacan baki ya kaure tsakaninsu wanda sauran Karuwai suka goya wa Cherish baya ,ganin haka ya sa yarsandar ta je ta dawo da sauran yansanda aka kama Cherish kuma aka kaita caji ofis daga bisani aka kai ta Kotu.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Sajen yarsanda ta sha duka a hannun wata karuwa a garin Lagos Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama