Yankuna 2 na yan tawaye sun fada hannun sojojin kasar Syria

Sojin Syria sun kwace iko da wasu yankuna biyu daga hannun 'yan tawayen kasar da ke wajen birnin Damascus a yammacin yau Asabar bayan wasu jerin hare-hare da luguden wuta ta sama da suka tilastawa daruruwan fararen hula tserewa daga yankin.
Sojin Syria bisa taimakon sojin kawancen kasashen Rasha sun kwace yankunan Kafr Batna da Sabqa daga hannun 'yan tawayen a dai dai lokacin da dubban fararen hula ke ci gaba da ficewa daga kasar don tsira da rayukansu.

Kawo yanzu dai gwamnatin Syria na rike da kimanin kashi 80 cikin dari na yankunan da ke hannun 'yan tawayen a bayatun bayan luguden wutar da ta kaddamar a ranar 18 ga watan  Fabarairun da ya gabata.

Masu sanya idanu kan rikicin na Syria sun ce 'yan tawayen gwamnatin yanzu sun kasu zuwa gida uku yayinda kowanne ke ikirarin iko da wani bangare a yankunan da suka rage a hannunsu.

Daga cikin bangarorin 'yan tawayen a cewar hukumar kare hakkin dan adam ta Birtaniya da ke sanya ido kan rikicin na Syria, akwai 'yan tawayen Faylaq al-Rehman da Jaish al-Islam da kuma Ahrar al-Sham wadanda ke da mayaka fiye da dubu 8, sai dai dukkaninsu bayan luguden wutar na yau sun dawo basa iko da komi face wasu tsiraran yankuna.

Kawo yanzu dai adadin farern hular da suka mutu tun bayan fara luguden wutar a cikin kasa da watanni biyu sun kai fiye da Mutane dubu daya da dari hudu.
Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

RFI
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN