• Labaran yau

  "Yan Najeriya na kukan babu yan Majalisa na wadata cikin miliyoyin naira"


  Yan kasar Najeriya sun fusata matuka kan milyoyin Naira da 'yan majalisar dokokin kasarsu ke karba a matsayin albashi,a daidai lokacin da al'uma ke cikin halin kaka-ni-kayi.

  A 'yan kwanakin da suka gabata, daya daga cikin sanatocin Najeriya,Shehu Sani wanda ke wakiltar al'umar Kaduna da ke arewa masu yammacin kasar, ya bayyana cewa 'yan majalisar dokokin kasarsa na karbar albashin akalla dalar Amurka 35.500 (Naira milyan 13.5).

  Abinda ya bakanta wa talakawan Najeriya wadanda ke kuka babu,inda tuni zazzafan cece-kuce suka barke a kafafan yada labarai da shafukan sada zumunta.

  Daya da cikin manyan masana a fannin tattalin arzikin Najeriya Odilim Energet ya ce :
  "Bai kamata ba mu bai wa 'yan majalisar kasarmu wuka da nama wajen yanka wa kansu albashi san ranu"

  Wani ma'aikacin gwamnati da ke Abuja babban birnin Tarayya,Usman Muhammad ya ce 

  "Babban kunya ace 'yan majalisar na karbar irin wannan albashin a daidai lokacin yawanci al'umarmu ke fama da fatara"

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

  TRT
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: "Yan Najeriya na kukan babu yan Majalisa na wadata cikin miliyoyin naira" Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama