• Labaran yau

  Wani mutum da ke auren maciji ya mutu sakamakon saran maciji

  Dan kasar Malaysia din nan da ya yi suna saboda basirarsa ta iya wasa da macizai ya mutu bayan wani gamsheka ya sare shi.

  Abu Zarin Hussin, wanda ma'aikacin kashe gobara ne, ya yi fice ne bayan wasu jaridun Burtaniya sun wallafa labaran da ke cewa shi dan kasar Thailand ne da ya auri macijiya.

  Mr Hussin ya bai wa sauran ma'aikatan kashe gobara horo kan yadda za su iya sarrafa macizai.
  Ranar Litinin aka kwantar da shi a asibiti bayan macijiyar ta sare shi lokacin da suke aikin kama macizai.

  Jairdar The star da ake wallafawa a kasar ta ce mutumin, dan shekara 33 wanda ke zaune a jihar Pahang, yakan koya wa takwarorinsa yadda za su gane nau'uklan macizai daban-daban kuma yana kama su ko da yaushe ba tare da ya kashe su ba.

  Ya taba fitowa a wani shirin talbijin da ke tattaunawa da hazikan mutane, Asia's Got Talent, inda aka nuna shi ya sumbaci wani macijin.

  A 2016, wani labari da kafofin watsa labaran Thailand- da ma na Burtaniya - ya ce Mr Hussin dan kasar Thailand ne da ya auri wata macijiya, yana mai cewa "budurwarsa" wacce ta mutu ta dawo a siffar maciji.


  An yi amfani da hotunan da Mr Hussin ke wallafawa a shafinsa na sada zumunta wurin gina labarin da ke nuna shi yana wasa da macizai.

  Mr Hussin, wanda ya ajiye macizai hudu a gidansa domin fahimtar halayensu, ya taba shaida wa manema labarai cewa: "Sun yi amfani da hotunana domin wallafa labaran kanzon-kurege cewa na auri macijiya."

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

  Daga BBC
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Wani mutum da ke auren maciji ya mutu sakamakon saran maciji Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama