• Labaran yau

  "Mai yunkurin yi wa Islam kwaskwarima, makiyin Allah ne"

  Mataimakin firaministan kasar Turkiyya,Bekir Bozdağ ya ce Islam addini ne da bai bukatan a yi masa kwalliya, saboda yana iya warware dukannin matsalolin da muke fuskanta har ya zuwa karshen duniya.

  Bekir ya furta wadannan kalaman don yi wa wadanda ke ikrarin cewa ya kamata a ce Musulunci ya bi rawar zamaninmu na yau,inda ya ce :

  "Rayuwarmu ta yau ce ya kamata a ce ta hau kan turbar Islam, ba wai akasin haka ba.A Addininmu komai a bayyane yake, babu ragi babu kari, ko dauka ko ka bari,Haka zalika babu tsaka-tsakiya.Batun yi mata kwaskwarima kuma, bai ma taso ba".


  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

  TRT 
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: "Mai yunkurin yi wa Islam kwaskwarima, makiyin Allah ne" Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama