Yadda Likita ya yi wa diyar mara lafiya ciki, ya ki amsar jariri

Ana zargin wani Likita mai suna Dr. Seyi ya yi ma wata yarinya yar shekara 16 ciki. Yarinyar mai suna Fatima Yusuf tana jinyar Mahaifiyarta ce wacce take fama da matsanancin ciwon suga kuma aka kwantar da ita a FMC Bida.Fatima ta rasu ranar Litinin bayan ta haifi jariri.

The Nation ta ruwaito cewa kafin rasuwar yarinyar ta shaida wa iyayen ta cewa Likitan ne ya yi mata fyade bayan ya kira ta zuwa cikin ofishinsa wanda ta bi shi bisa tunanin cewa zance ne zai yi mata dangane da rashin lafiyar mahaifiyarta.Amma daga shigarta ofishin sa sai ya taushe ta ya biya bukatarsa kuma daga lokacin ne ya ci gaba da aikata lalata da ita.

Wata majiya ta labarta cewa yarinyar ta ce Likitan ne ya yi mata ciki amma Likitan ya musanta haka.Lamarin ya sa ala tilas Sarkin Bida Alh. Abubakar Yahaya ya sa baki inda ya bukaci a yi wasu gwaje-gwaje bayan Likitan ya ce shi dai ya rungume ta ne a cikin ofishinsa, amma bai yi lalata da yarinyar ba.

Yanzu haka hukumar da lamarin ya shafa ta shigo cikin lamarin tare da Lauyoyin hukumar wadanda tuni suka shiga tara bayanai kuma hukumomi suna ci gaba da bincike.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN