Masarautar Zuru a karshen mako, yadda taron BBSO ya kasance

An bude ofishin kungiyar Buhari Bagudu Support Organization (BBSO) na Zuru Zone a garin Zuru.
Manyan Mutane da dama suka yi jawabai a wurin taron daga cikinsu akwai Mataimakin Shugaban Jama'iyar APC na Jaha Alh Abubakar Kana da Shugabannin Jama'iyar na kananan hukumomun Jega,Maiyama.Zuru. Fakai. Da kuma Chiyamomin mulki na Jega Ngaskida da saurasu

Haka Alh Bello Doya, Yariman Zuru Alh Sadiq Sani Sami Shugabam Mata ta APC ta zone da BBSO ta Jaha kuma dukansu sunyi magana ne akan ayukka na Shugaban Kasa da Gwamnan Jiha.

A nasa jawabi shugaban kungiyar na Jiha Alh. Umar Altine Danfari Suru ya jaddada wannan kungiya tana aikine a karkashin Jama'iyar APC .

Shi kuma Alh. Faruku Musa Yaro Inabo godiya yayi ga Allah tare da salati ga Manzon tsira ya kara da yabawa jama'ar kasar Zuru akan goyon bayan da suke ba Gwamnatin Sen. Atiku Bagudu daganan ya kara kira da aci gaba da bada hadin kai haka ya fadi sabbin ayuka ciki har da Ginin Fadar kasar Zuru da aka fara Sannan ya bada tallafi na kananan sanao'i ga mata arbain da daya (41) wato a kowane gunduma (Ward).

Daga Abba Muhammed

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN