Dan peace corps ya kashe kansa sakamakon rashin aminta da dokar PCN

Ana zargin cewa wani mutum ya kashe kansa saboda shugaba Muhammadu Buhari bai sa hannu a dokar kafa rundunar Peace Corps Nigeria (PCN) ba wadda Majalisar Wakilai ta Najeriya ta gabatar wa shugaban kasa.

Wannan jawabin ya fito ne daga bakin wani dan takaran kujerar shugaban kasa a jam'iyar National Conscience Party NCP Dr. Thomasa Wilson Ikubese kuma ya bukaci shugaba Buhari ya sake duba lamarin .

Dr. Thomas ya kara da cewa wanda ya mutu Mr. Gambo Timothy Dogo dan garin Nappe ne a karamar hukumar Dukku a jihar Gombe ana zargin cewa ya kashe kansa ne sakamakon ranshin amintar shugaba Buhari da dokar kafa PCN bisa dalilai na tsaro da rashin kudin gudanar da rundunar.
 
Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN