• Labaran yau


  Yadda aka dambace tsakanin soji, yansanda da jami'an FRSC a Abuja.

  Bayanai daga birnin Abuja sun nuna cewa an sami hatsaniya tsakanin Sojoji, yansanda da kuma jami'an kiyaye hadurra na kasa FRSC, bayanai sun nuna cewa matsalar ta taso ne bayan yansanda da ke aiki da AEPB suka yi kokarin bayar da takarda a hukumnance ga ofishin FRSC da ke Wuse zone 7.

  Rahotanni sun yi zargin cewa soji da yansanda da ke aiki da AEPB sun dan lallasa wata jami'ar FRSC wanda ya haddasa fito na fito tsakanin jami'an.


  Wasu bayanai sun nuna cewa an raunata wani soja a lokacin fadar yayin da jami'an FRSC suka yi garkuwa da daya daga cikin jami'an AEPB.

  Su kuma jami'an soji da yansanda suka kama jami'in FRSC guda daya suka yi garkuwa da shi.

  Bayanai sun ce dukanin bangarorin guda biyu sun ja daga ta hanyar bukatar daya bangaren ya fara sako wanda ya kama.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda aka dambace tsakanin soji, yansanda da jami'an FRSC a Abuja. Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama