• Labaran yau


  Yombe ya bayar da mota 11 ga jama'ar Zuru domin kaunar Gwamna Bagudu

  A ci gaba da kyautatawa da ya saba tare da mayar da hankali ga bukatun al'ummar kasarsa ta Zuru, Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai ya sake bayar da kyautar karin wasu motoci ga jama'ar kasar Zuru.

  Wadanda suka more wannan damar sun yaba tare da nuna godiya ga Mai girma Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Baguda tare da Mataimakinsa Alh. Samaila Yombe Dabai wanda a cewarsu a cikin tunaninsa Allah ya kadari suka amfana da wannan kyautar.

  Idan baku manata ba, Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Samaila Yombe yana ta bayar da kyautukan motoci tare da tallafi ga jama'ar Mazabarsa ta Zuru.

  A nashi jawabi a wajen takaitaccen bikin mika motocin ga jama'arsa, Mataimaikin Gwamna Alh. Samaila Yombe ya ce ya yi wannan kyautar ne saboda jin dakin shugabancin Gwamanan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu a matsayin Gwamnan jihar Kebbi.

  "Gwamna Atiku Bagudu ya fitar da mu kunya domin ya yi abin da muka rantse cewa zamu yi domin da aka rantsar da mu ya yi alkawurra da yawa bisa ababe da za a yi kuma tabbas an yi.Kuma duk wanda ke a nan wajen a yau ya shaida abin da Gwamna Bagudu ya yi.Sakamakon farin cikin haka ya sa na bayar da wadannan motoci saboda in bayar da kwarin guiwa domin a taimaka domin ya dawo shigabanci a karo na biyu da yardar Allah".

  Daga Isyaku Garba

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yombe ya bayar da mota 11 ga jama'ar Zuru domin kaunar Gwamna Bagudu Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama