• Labaran yau


  Wani dansanda ya kashe soja bayan zafafar cacan baki

  An sami wata yar hatsaniya yayin da wani jami'in dansanda wanda ke aikin tsaro a kamfanin mai na Shell Petroleum da ke Odimodi a jihar Delta ya harbe wani jami'in soji da suke aikin hadin guiwa tare da shi har lahira sakamakon wata zafafar cacan baki da ta taso tsakaninsu.

  Punch ta labarta cewa jami'an guda biyu sun yi wata zafafar muhawwara ce tsakaninsu kuma sakamakon haka dansandan ya harbe sojan da bindiga wanda ya haifar da mutuwar sojan nan take.

  Ganin haka ke da wuya sai dansandan ya dauke bindigar sojan ya ruga da gudu kuma yana ta harbi a sama lamari da ya tsoratar da mazauna garin na Odimodi.

  Daga bisani jami'an tsaro na hadin guiwa sun zo suka dauki gawar sojan.

  Kakakin hukumar yansanda na jihar Delta ya shaida wa manema labarai cewa zai tuntubi DPO na garin Odimodi daga bisani zai waiwayi manema labarai dangane da zancen.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Wani dansanda ya kashe soja bayan zafafar cacan baki Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama