Hizbah ba ta da karfin ture sojoji domin ta gudanar da aikinta - Daurawa

Shugaban hukumar Hizbah na jihar Kano Malam Aminu Daurawa ya ce jami'an hukumarsa basu da hurumin ture jami'an tsaro kamar soja,yansanda ko SSS domin su hana bidi'a da aka aikata a lokacin bikin daurin auren diyar Gwamna jihar Kano Umar Ganduje.

Daurawa ya kara da cewa fiye da ma'aurata 100 ne suka cashe ayarsu a lokutan aure a birnin Kano kafin aukuwar bikin auren diyar Ganduje.

Ya kuma ce mutane suna kunnen kashi bisa shawara da Hisbah ke basu kuma da yawan lokaci jami'an Hisbah kan ci karo da sojoji a bakin kofar gidan da ake biki da ya shafi kade kade da raye raye amma ba yadda jami'an Hizbah za su ture soja .

Daurawa ya ce duk da yake baya cikin garin Kano a lokacin da lamarin ya faru amma ko da yana nan Hukumarsa ba ta da karfin da za ta iya hana diyar Ganduje daga gudanar da bikin.Sakamako haka ya ce sai ya rungumi "yin shiru" a kan lamarin bisa la'akari da shawara da Malaminsa ya bashi kuma shi mai biyayya ne ga Malamansa a gefe daya kuma yan jarida sun sa shi gaba..

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN