• Labaran yau


  Kalli dansanda da ya jagoranci sata a gidan mataimakin gwamnan Jigawa

  Hukumar yansanda a jihar Kano ta kama wani sajen na yansanda mai suna Sgt.Sani Danjuma tare da wasu mutum uku bisa zargin sata a gidan mataimakin gwamnan jihar Jigawa Abubakar Hadejia.

  Kakakin hukumar yansanda na jihar Kano Magaji Majiya ne ya shaida wa manema labarai haka a hedikwatar yansanda da ke Kano ranar Talata.Ya kuma ce rundunar ta kori Sgt.Sani Danjuma daga aikin dansanda.

  Wadanda aka kama sun hada da  Nura Ahmed, Abdullahi Ahmed and Abubakar Uzairu.

  Kakakin na yansanda ya ce za a gurfanar da su a gaban Kotu da zarar an kammala bincike.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kalli dansanda da ya jagoranci sata a gidan mataimakin gwamnan Jigawa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama