• Labaran yau


  An bindige masu garkuwa da mutane domin karban kudin fansa

  Dubun wadansu matasa guda shida ya cika bayan yan sanda sun bindige su har lahira sakamokon addabar jama'ar garin Agbor da suka yi ta hanyar sace mutane su yi garkuwa da su domin karbar kudin fansa a jihar Delta.

  Jihar Delta dai tana daya daga cikin jihohin Najeriya mafi hadari wajen satar mutane domin a yi garkuwa da su. Lamari da ya zama kalubale ga hukumar yansanda na jihar wadda jami'an ta ke kokari wajen ganin sun dakile irin wadannan matsalar.

  Kawo yanzu dai ba'a ambato sunayen mutanen ba haka zalika hukumar yansanda na jihar Delta bata yi bayani ba kafin lokacin wallafa wannan labarin.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An bindige masu garkuwa da mutane domin karban kudin fansa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama