Maryam Sanda ta shirya birthday na diyarta bayan fitowa daga kurkuku

Maryam Sanda wacce ta kashe mijinta Bilyamin kuma wata Kotu a birnin Abuja ta bayar da belin ta ta gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwar diyarta .

Kotu ta tasa keyar Maryam zuwa Kurkuku bayan an zarge ta da kashe mijinta Bilyamin Muhammed Bello a watan Nuwamba na bara.Amma Kotu ta bayar da belinta ranar Laraba 7 ga watan Maris bayan an gabatar da takardar Asibiti da ya nuna cewa tana dauke da juna biyu kuma bata da lafiya.

Rahotanni sun nuna cewa jim kadan bayan fitowarta daga Kurkuku, Maryam ta shirya wannan bikin zagayowar ranar haihuwar diyarta Alisha. Ta shirya bikin ne a gidan mahaifiyarta kuma yan uwa da abokan arziki ne suka halarci bikin.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN