Gwamna Bagudu masoyin Fulani ne - Shugaban karamar hukumar Zuru

An nada sabon shugaban al'ummar Fulani na kasar Zuru tare da sauran zababbun shugabannin Fulani su 13 a wani taro da aka gudanar a dakin taro na Komo Unity Hall Zuru.Sabon shugaban Fulani na kasar Zuru shi ne Alh.Abubakar Aliyu wanda aka fi sani da suna Abiola.

Shugaban karamar hukumar Zuru Alh. Muhammed Kabir Abubakar tare da wakilai daga kungiyar Miyetti Allah na jihar Kebbi da sauran masu ruwa da tsaki a jam'iyar APC na Zuru , shugaban ya mika takardar shaida ga sabon shugaban Fulani.

Shugaban karamar hukumar Zuru Alh. Kabir Abubakar ya ce Mai girma Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu masoyin al'ummar Fulani ne, yace Gwamna Bagudu tare da hadin guiwa da wani kamfanin yin Madara a jihar Oyo ya zagaya cikin Fulani domin samar da shiri da zai sa a dinga sayen nonon shanu daga wajen Fulani a Rugga domin Kamfanin ya dinga sarrafa nonon zuwa Madarar zamani.

Haka zalika shugaban ya ce Gwamna Bagudu ya bukaci Fulani su dinga sa yaransu a makaranta, ya kuma kara da cewa Gwamna ya ce Fulani su sami takamammen wuri su zauna domin Gwamnati ta tsara yadda za ta taimaka masu.

Daga cikin manya da suka halarci taron sun hada da Alh. Usman Ankwai, Alh. Abdullahi Rago, Alh Gado mai radio da sauran manyan baki.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN