B-kebbi: Mata ta banka wuta a gidan miji sakamakon kishi a Badariya

Mazauna unguwar Badariya da ke garin Birnin kebbi sun wayi gari cikin mamaki ganin yadda tsananin kishi  ya sa wata mata mai suna Zainab ta banka wuta a gidan mijinta mai suna Yunusa wai domin ta sami labarin cewa zai yi mata kishiya ta hanyar auren wata mai suna Aisha.

Wata majiya ta shaida wa wani dan jarida cewa lamarin ya basu mamaki sakamakon yadda matar ta aikata wannan aiki. Majiyar ta kara da cewa akwai radi-radin cewa Yunusa yana shirin kara mata ne mai suna Aisha a karshen mako.

Kakakin hukumar yansanda na jihar Kebbi DSP Suleiman Mustapha ya shaida mana ta wayar salula cewa babu wanda ya kawo koke ko ya shaida wa ofishin yansanda da ke garin Birnin kebbi aukuwar wannan lamari kawo yanzu.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN