Mai gadin Chochi ya yi wa yar shekara 20 fyade

Ana zargin wani mai gadin Chochin Katolika na Sacred Heart a Uwani na garin  Enugu da yi wa wata yarinya yar shekara 20 fyaade bayan ya taushe ta a wani lungu a Chochin kuma ya biya bukatarsa.

Yanzu haka an kai yarinyar wani Asibiti inda wani Lokita ya tabbatar da aikata gyade ga yarinyar yace ana fargaban ko yarinyar ta kamu da cutuka da ake iya daukawa ta hanyar jima'i ganin cewa mai gadin bai yi amfani da kariya na kororon roba ba.

Haka zalika likitan ya ce ko da an yi mata gwajin cutukan da ake samu ta hanyar jima'i ba zai nuna sakamako cewa tana dauke da shi ba ganin cewa lamarin ya faru ne ba da dadewa ba.

Amma ya bukaci a kawo mai gadin domin a yi masa gwajin HIV wanda ya ce ta haka ne za a gane ko yarinyar ta kamu da cutar ta haka za a iya ba ta taimakon gaggawa.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN