Dan giya ya mutu bayan ya kwankwadi maganin kwari cikin kuskure

Wani dan giya ya mutu bayan ya kwankwadi maganin kwari bisa tunanin cewa ruwa ne kuma sakamakon haka ya mutu a wani gidan cin abinci na Chinese Restaurant a unguwar Adeniran Ogunsanya da ke Surulere a birnin Lagos.

Majiyar mu ta labarta mana cewa mamacin wanda ya fito daga wajen bukin aure tare da abokansa a Aguda na Surulere ya iso gidan cin abincin bayan ya shayu da barasa.Daga isowarsa ya bukaci a ba shi ruwa da abinci amma sai ya ga wani roban ruwa a kan tebur wanda wani ma'aikacin gidan abincin ya ajiye ba tare  da sanin cewa maganin kwari ne a ciki ba shi kuma sai ya kwankwade maganin.

Bayan ya kwankwadi maganin ne sai ya shaida wa abokansa cewa ya sha wani abu da bai san ko miye ba a cikin robar ruwa da aka ajiye a kan teburin abinci.Sakamakon haka aka garzaya da shi zuwa wani asibiti amma rai ya yi halinsa.

Yansanda daga caji ofis na Bode Thomas sun kama Manajan gidan cin abincin kuma suna gudanar da bincike.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN