Ko ka san shan ruwa a tsaye zai iya haifar maka da matsala ?

Yawancin mu mun taso da sanin cewa shan ruwa a tsaye ba shi da kyau, sai dai da yawa na watsar da wannan koyarwar da zaran sun girma. Dalili kuwa bai wuce rashin sanin alfanun yin hakan ba, inda wasu ma ke tunanin batun ba shi da tushe.

A dan binciken da na yi, na gano cewa shan ruwa a tsaye yana da matukar hatsari ga lafiyar jiki.
Masana na da ra’ayin cewa ba a samun alfanun shan ruwa har sai an yi shi a zaune, kuma a hankali, ba a kwankwade ba kamar yadda muke yi yawancin lokuta.

Sun kuma zayyano irin hatsarin da ke tattare da yin sabanin haka, ga wasu daga ciki:

1. Ciwon Gabobi: duk mai shan ruwa a tsaye na fuskantar barazanar kamuwa da ciwon gabobi musammam ma a lokacin tsufa. Wannan ya na faruwa ne a sakamakon ruwa da ya ke taruwa a gabobin fiye da yadda ya kamata.

2. Rashin Kashe kishi: bayan mutun ya sha ruwa a tsaye, nan da nan zai sake jin wani kishi.

3. Matsala ga koda ko mafitsara: koda ba ta iya tace ruwan da aka sha a tsaye yadda ya kamata. Wannan ya na sanya wa dauda da ke cikin ruwan ya makale a kodar, al’amarin da ka iya haifar da matsalolin mafitsara ko kuma ciwon koda.

4. Zai iya haifar da gyambon ciki (Ulcer) da kwarnafi (heart burn): A yayin da aka sha ruwa a tsaye, musamman ma idan kwankwada aka yi da sauri, ruwan zai bugi bututun da ke hade da baki da ciki da karfi, ya kuma bugi bangon cikin. Wannan ya na sa sinadarin acid da ke cikin ya dawo cikin bututun, al’amarin da idan ya ci gaba da faruwa, ka iya haifar da kwarnafi, da kuma gyambon ciki

 5. Ya na hana abinci narkewa da wuri: Yayin da muke zaune ne jijiyoyin jikin mu ke iya samun nutsuwar narkar da abinci da wuri. Yayin da muke tsaye kuwa, yanayin da muke ciki ba irin wanda zai inganta haka ba ne

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Daga Alummata
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN