• Labaran yau


  Wani mutum ya yi wa yansanda 4 mugun duka a Lagos

  An kwantar da wadansu yansanda guda hudu a Asibiti sakamakon raunuka da suka samu bayan wani mutum mai suna Afeez Olalekan ya yi masu duka kuma ya kwace gidan harsashi na bindigar AK47 daga hannun yansandan. Wadanda suka sha duka a hannun Afeez su ne ASP Rufai Sulaimon, Sgt Obijimo Ihenyichuku and two Inspectors- Anthony Akowe and Godspower David.Yansandan suna aiki ne a ofishin yansanda na Bar Beach a garin Lagos.

  Majiyar mu ta labarta cewa lamarin ya faru ne bayan wani mutum mai suna Ahmed Ogunremi ya yi karan Afeez a wajen yansanda, lamari da ya sa suka je domin a tafi da Afeez, amma sai ya ki daga bisani ya fasa kwaalba ya yi masu rauni .

  Daga karshe dai an kama Afeez kuma aka gurfanar da shi a gaban wata Kotun Majistare a Ikeja inda Afeez ya ki ya amsa laifinsa. Sakamakon haka Alkalin Kotun  Mrs. O.A. Layinka ta dage shari'ar har
  zuwa ranar 16 ga watan Aprilu bayan ta bayar da belin Afeez a kan N200.000 amma an tasa keyar Afeez zuwa Kurkuku kafin ya cika ka'idar beli.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Wani mutum ya yi wa yansanda 4 mugun duka a Lagos Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama