Gwamnatin jihar Kebbi za ta kashe N50m wajen inganta harkar wasanni

Gwamnatin jihar Kebbi ta aminta da kafa kungiyar kwallon kafa na jiha da aka sa wa suna Kebbi United Football Club wacce za ta wakilci jihar Kebbi a matakin kwallon kafa na kasa.Haka zalika gwamnati jiha za ta bayar da Naira miliyan arba'in da daya N41m domin bayar da dama kungiyar ta taka rawa a wasanni a mataki na kasa.

Bugu da kari gwamnati za ta kashe N9.8m domin inganta filin wasa na Haliru Abdu da ke garin Birnin Kebbi.

Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya aminta, domin gwamnatin jihar Kebbi za ta dauki nauyin yara 10 da suka nuna hazaka da kwarewa a wani shiri da aka gudanar na zakulo hazikan matasa yan kwallo kuma za su tafi makarantar koyon dabarun kwallon kafa a Illorin na jihar Kwara.

Daga Isyaku Garba

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN