• Labaran yau


  Ko ka san miye zai faru idan shugaba Buhari bai tsaya takara ba a 2019 ?

  Gwamnan jihar Niger Abubakar Sani Bello ya ce tattalin arziken Najeriya zai tabarbare matukar shugaba Buhari bai sake tsayawa takara a zaben 2019 ba.

  Gwamnan wanda yake neman goyon bayan jama'a domin su sake zaban shugaba Buhari a 2019 ya ce 'yan Najeriya ba za su yi nadama ba idan suka sake zaben shugaba Buhari a 2019.

  Ya ce idan aka sake zaben shugaba Buhari tattalin arzikin Najeriya zai inganta kuma zai kasance a mizali madaidaici.

  Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a gidan Gwamnati a birnin Minna yayin da ya karbi mutanen garin Kontagora a fadar gidan gwamnati a karshen mako.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ko ka san miye zai faru idan shugaba Buhari bai tsaya takara ba a 2019 ? Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama