• Labaran yau

  Kamen dan jarida: Yan wata kungiya za su mamaye ofishin DSS a Abuja

  Wata kungiya mai suna mumudondo wacce ke fafutukar ganin an saki Mr. Anthony Ezimakor wanda shi ne babban jami'n kanfanin jaridar Daily Indipendent a Abuja da ake zargin cewa hukumar DSS ta damke shi kuma tana tsare da shi ta ce za ta mamaye ofishin hukumar DSS a Maitama birnin Abuja ranar 7 ga watan Maris 2018 daga karfe 9:00 na safe.

  A wata sanarwa da shugaban kungiyar ya sa wa hannu kuma ya raba wa manema labarai aka wallafa a shafukan yanar gizo Charles Oputa ya yi zargi cewa suna fafutukar ganin cewa an saki dan jaridar ko a kai shi Kotu domin ya sami sukunin kare kansa domin ganin an kauce wa maimaita irin yanayi da Sheikh El-zakzaky ya sami kansa a karkashin hukumar ta DSS a Abuja .

  Ya kuma roki kafafen watsa labarai na kasashen waje da na Najeriya su sa ido ta hanyar kasancewa a wajen ranar 7 ga wata Maris.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kamen dan jarida: Yan wata kungiya za su mamaye ofishin DSS a Abuja Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama