Dokar kafa peace corps, yan majalisa sun fara shirin kalubalantar shugaba Buhari

Wasu yan Majalisar Wakilai su hudu sun fara aikin tattara sa hannu na yan Majalisar Wakilai domin ganin cewa sun tabbatar da dokar kafa rundunar Peace Corps wanda shugaba Buhari ya ki sa hannu, yan Majalisar suna tattara sa hannun ne domin ganin sun kawar da ikon shugaban kasa kan lamarin .

Wani bincike da New Telegraph ta kaddamar ya nuna cewa yanzu haka yan Majalisar sun hada sa hannu daga yan'uwansu 173, ana bukatar sa hannun yan Majalisa 240 a Majalisar Wakilai yayin da akke bukatar sa hannun mutum 81 daga Majalisar Dattawa domin tilasta dokar ko duk da yake shugabn kasa bai amin ta ba.

An sami wani rahotu daga jihar Taraba wanda ya alakanta mutuwar wani mutum da aka ce ya kashe kanshi sakamakon rashin aminta da dokar kafa Peace Corps da shugaba Buhari ya yi.

Amma shuga Muhammadu Buhari ya ce bai sa hannu a dokar kafa Peace Corps ba ne bisa dalilai na rashin kudi da za'a tafiyar da rundunar da kuma kasancewa aiyyukan rundunar ka iya zama kalubale ga aikin wasu rundunonin tsaro da ake da su a yanzu.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN