Kungiyar da ke karadin ci gaban jihar Kebbi watau Kebbi Development Forum ranar Laraba ta gudanar da taron bita na tattaunawa akan masu ruwa da tsaki kan inganta da tsabtace abinci . Maudu'in tattaunawar an gudanar da shi ne bisa tuntuba da bayanai daga masana,Malamai, yan jarida tare da kwararru daga wasu sassa na ayyukan gwamnati.
An mayar da hankali wajen zakulowa tare da bayar da shawara kan ababen da ke haddasa matsalolin tsabta a wajen sana'oi da kuma gidajen jama'a.
An ambaci cewa wasu da ke shigowa birane misali garin Birnin kebbi domin Almajiranci ko gudanar da sana'a galibi sukan kama shaguna ne a matsayin wajajen barci marmakin gidajen haya, sakamakon haka da dare domin rashin ban daki ko wajajen bahaya sukan je gota da gwamnati ta yi sai su yi bahaya a ciki wanda hakan yakan haifar da yanayi na rashin tsabta.
Haka zalika an ambata yadda wasu gidaje ke mayar da gota wajen zuba shara, wanda wasu masu jawabi suka alakanta faruwar haka da rashin samar ta takamammen wajen zuba shara , misali a garin Birnin kebbi gwamnati bata samar da wajajen zuba shara ba sakamakon haka jama'a ke yin abin da suka gan dama dangane da lamarin shara.
Tattaunawar ta kuma fadada bayanai a kan yadda ake gudanar da wasu sana'ai kusa da wajen kazanta ba tare da la'akari da yadda hakan zai iya shafan lafiyar al'umma ba.
Daga karshe an nada kwamitoci guda hudu bisa tsarin masana wanda suka yi nazari akan maudu'in lamarin taron kuma suka bayar da shawarwari akan yadda za'a sami mafita domin a samar da yanayi mai tsabta wajen gudanar da sana'oi da zamantakewa a fadin jihar Kebbi.
Daga Isyaku Garba.
Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Tags:
BIRNIN-KEBBI